Kalli Yadda Aka Kama Wani Dan Sanda Yana Lalata Da Mai Cutar Korona A Wajen Da Aka Killace Mata - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Kalli Yadda Aka Kama Wani Dan Sanda Yana Lalata Da Mai Cutar Korona A Wajen Da Aka Killace Mata


Asirin wani jami'in dan sanda ya tonu a yayinda akayi nasarar kama shi yana lalata da Mai cutar covid19 , a wurin da aka killace mata masu dauke da cutar ta covid19.

An kama jami'in dan sandan mai matsakaitan shekaru ne a daidai lokacinda yake lalata tareda wata mai cutar covid19 da aka killaceta a wani sansani na killace mata masu cutar ta korona dake Busia.

Kasancewar an rarraba jami'an tsoro na yan sanda tareda jami'an hukumar gyaran hali a sansanin na killace mata masu dauke da cutar ta korona inda aka hada kowane Dan sanda tareda jami'in hukumar gyaran hali domin suyi aiki a tare.

Saidai a ranar alhamis dinda ta gabata da misalin karfe 10pm na daren ranar ne wani konstable din Dan sanda mai suna Emmanuel Ng’etich, yafara hira da wata mai cutar korona, wanda hakan ya tunzura abokin aikinsa Jeff Obondo, yatafi wurin sauran jami'an su domin shaida masu abinda Emmanuel yakeyi.


Bayan ya sanar da jami'an ne,  sai dikkanin jami'an suka tashi domin ganewa idonsu abunda ke faruwa, saidai fa basuga Ng’etich, tareda matar mai cutar korona ba,  wanda hakan ya tayar masu da hankali matuka.


Wannan lamari ya daga masu hankali hakan yasa suka shiga binciken lunguna da sakunan dik da ke cikin gidan,  Kwatsam sai suka fara jin hayaniya .


Jami'an yan sanda sunyi hanzarin shiga bangaren da aka killace mata masu cutar ta korona inda suka tarar da dikkanin matan da aka killace a waje suna korafin cewa Dan sandan mai suna Ng’etich yana nan yana yiwa Wata budurwa fyade.


Hukumomin sun bayyana cewa bayan sun shiga sansanin inda aka killace mata masu dauke da cutar ta korona ne,  suka tarar da Ng’etich tareda budurwar mai cutar korona a tsirara suna lalata.

Drop Your Comment

0 Comments