Jarabawar da take yawo a yanar gizo ta jabuce inji hukumar Waec - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Jarabawar da take yawo a yanar gizo ta jabuce inji hukumar WaecHukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantar Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC ta gargaɗi ɗalibai cewa satar amsar Jarrabawar Lissafi da ke yawo a shafukan sada zumunta ta jabu ce.
Hukumar WAEC ta shaida wa sashen Pidgin na BBC cewa masu zamba ne suka samar da irin waɗannan takardun jabun inda suke so su yi amfani da su don karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane.
A yau Litinin ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Najeriya ke soma rubuta jarrabawarsu ta kammala karatu bayan da aka samu jinkiri na watanni saboda annobar cutar korona.
Ɗalibai fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makwanni suna rubuta jarrabawar da ake kira WAEC wadda kuma a kan yi a wasu ƙasashen yammacin Afirka.
''Duk wani ɗalibi da ya karɓi takardun jabun zai sha mamaki a yayin da ya shiga ɗakin jarrabaw ya ga ta sha bamban da wacce za a ba shi,'' in ji WAEC.
Mai magana Hukumar da yawun WAEC Demianus Ojijeogu ya ce ɗliban Ghana ba su zana jarrabawar Lissafi ta WAEC ta bana ba kamar yadda mutane ke faɗa.
WAEC ta faɗi haka ne bayan da aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa irin tambayoyin da aka yi w ɗaliban Ghana ne za a yi wa na Najeriya a takardar jarrabawar.
"Na ga takardu uku na jabu a jiya,'' in ji Mr. Ojijeogu.

Drop Your Comment

0 Comments