Dokar Danna Waya kana Tafiya Ta Tabbata - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Dokar Danna Waya kana Tafiya Ta Tabbata


A duk lokacin da matafiya suka sauka daga jirgin ƙasa a garin Yamato, abin da za su fara cin karo da shi a tashar jirgin shi ne wata alama da ke nuna haramcin amfani da waya yayin da ake tafiya a ƙafa a kan titi.
Garin Yamato na da nisan kilomita 30 daga Tokyo babban birnin ƙasar Japan.
Wannan dokar da aka saka, jami'an ƙasar ne suka ƙirƙire ta - duk da ba a ɗaukar mataki mai tsanani ga waɗanda suka karya dokar.
Tilasta wa mutane daina latsa wayoyinsu yayin tafiya kan titi abu ne da ƙasashe da dama suke ke son a tabbatar.
Me ya sa hukumomi a Yamoto ke ganin wannan dokar da aka saka za ta iya sauya ɗabi'un mutanen garin?

'Akwai hatsari'

Tituna a Japan na cike da mutane da ake kira "arukisumātofon ", wanda hakan ke nufin masu tafiya suna latsa wayoyinsu. Wannan wata kalma ce inda aruki ke nufin (tafiya) sai kuma sumātofon na nufin (wayar zamani).
A watan Janairu, garin Yamato ya gudanar da bincike a wurare biyu inda aka gano cewa kashi 12 cikin 100 na mutum 6,000 da aka yi bincike a kansu suna latsa wayoyinsu yayin da suke tafiya kan tituna.
Magajin garin Satoru Ohki - wanda yana daga cikin wadanda suka shige gaba domin yin wannan doka - ya bayyana cewa hakan abu ne mai hatsari.


Tun da farko dai Mista Ohki ya bayar da shawarar yin wannan doka ga 'yan majalisa, bayan ya gama tuntuɓa sai ya gano cewa mutum takwas cikin 10 sun goyi bayan shawarar da ya kawo.
Bayan hakane a watan Yuni aka ƙaddamar da dokar hana latsa waya yayin da ake tafiya kan titi.
A kwanakin farko da aka fara amfani da wannan doka, garin na Yamato ya ɗauki ma'aikata da suke riƙe wasu alamu a hannunsu a daidai tashar jirgin ƙasar garin, alamun na ɗauke da bayanai da aka naɗa a faifan CD da ke bayani kan dokar.

Source: Bbc hausa

Drop Your Comment

0 Comments