Gwamnan abdullahi Ganduje na kano ya sanar da babu sassauci ga wanda duk gwamnatin sa ta kama na karban cin hanci da rasha. 

Cin hanci da rashawa wanda gwamnan ya kwatanta da mummunan abu yace ko kadan bazai bari gwamnatin sa tayi kasa a gwuiwa ba wajen kunyata masu karban cin hanci da rashawa ba.