An ja kunnen Shugaba Buhari kan dukiyar kasa - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

An ja kunnen Shugaba Buhari kan dukiyar kasa

Jam'iyar PDP ta bayyana ra'ayin ta na nuna son Shugaba Buhari ya hukunta duk wanda aka kama da satar kudin kasa kamar yaddam jam’iyyar PDP din ta bayyana cewa maganar shugaba Buhari ta tabbatar da abinda ta dade tana fada cewa akwai barayin dukiyar talakawa a Jam'iyar APC.

Ta kuma kara da cewa gwamnati na baiwa wadannan barayi kariya ta yadda ba a iya hukunta su.

Saidai PDP ta ce tana kira ga shugaban kasar da ya yi himma wajen hukunta wadannan maciya amanar.

Sakataren watsa labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce a baya PDP ta samar da hukumomin yaki da rashawa da cin hanci kuma ta hukunta wadanda aka kama da laifi.

Drop Your Comment

0 Comments