Yadda jama'a da yawa suka zamo attajirai sanadin yan N-Power - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Yadda jama'a da yawa suka zamo attajirai sanadin yan N-Power


Ministan jinkai da walwalar al'umma hajiya sadiya umar Farouq tace A ranar Juma’a 3 ga watan Yuli na gudanar da wani taron bitar kwasa-kwasan tare da wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin na Npower inda na gode musu saboda hidimarsu ga kasarmu suma Sun gode wa Shugaban kasar Muhammadu Buhari bisa wannan damar daya basu yau Ya kasance mako guda ke nan da aka bude Wajen samar da rajista ta @Npower don sauƙaƙe rajistar rukuni na C, sama da matasa miliyan 3 &  ne sukayi rijista A halin da ake ciki yanzu...

haka zalika kuma na yi farin cikin sanar da mahalartan taron namu na cewa kawo yanzu sama da mutane 109,000 wadanda suka amfana da N-Power wasu sun zama yan kasuwa & masu daukar ma'aikata aiki tun lokacin da aka kafa wannan shirin a 2016 don inganta tattalin arzikin & GDP. A ranar Juma'a 3 ga watan Yuli, Perm Sec Jalal Arabi ya kasance tare da ni don maraba da kwamitin.

Wannan babban dama ne ga wa'inda suka samu Aikin n-Power ko wa'inda zasu samu nan gaba da su yi kokari su ga sun amfana da kudaden da zasu samu tun kafin damar hakan ta kubce musu. Ana sa ran nan da yan watanni kadan za'A bayyana sunayen wa'inda suka samu nasarar samun aikin n-power da aka cika a karshen watan daya gabata.

Drop Your Comment

0 Comments