Yadda aka yi ma sarkin wani gari a Kebbi yankan rago - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Yadda aka yi ma sarkin wani gari a Kebbi yankan rago

Inda ranka zaka sha kallo gaba har yanzu miyagun nan basu kare ba, wannan wani sarki ne da aka yi masa yankan rago a jihar kebbi bayan yan ta'addan sun kamashi.

Kamar yadda shafin dokin karfe ta rahoto cewa;
Sarkin Bajida Musa Muhammad kenan wato (Uban ƙasar Bajida) dake karamar hukumar mulki ta Zuru dake jihar kebbi Wanda a jiya Talata wasu ƴan ta'adda suka kashe shi ta hanyar sara da adda.

Allah ya bawa iyalan sa hakurin rashi kuma anan ne muke mika kukan mu ga gwamnati da tayi wani abu akai domin ganin an kawo karshen zub da jinin da ake yi a fadin kasa.

Drop Your Comment

0 Comments