Nan da wata 7 Baza ku sake jin Labarin ta'addancin kungiyyar Boko Haram ba -Soji - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Nan da wata 7 Baza ku sake jin Labarin ta'addancin kungiyyar Boko Haram ba -SojiAbubakar sadeeq shugaban sojin saman Nigeria ya bayyana wa yan Nigeria susha kurumin su Boko Haram na dan nan da yan watanni ne zasu yi maganin ta za'a bar jin labarin ta kwata-kwata. 

Abubakar ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da sojojin na su a Maiduguri inda nanne ake fama da matsalar ta boko haram, ya kuma bayyana a yanzu kam sun samu kwarin gwuiwar yakar yan kungiyyar kuma ya karfafawa yaran nasa da su maida hankali a fada da kungiyar wajen ganin an kwao karshen ta.

Abubakar yace sun samu jiragen yaki 22 sannan kuma akwai 16 dake kan hanya. Yace wadannan jirage sun taimaka matuka wajan nasarorin da suke samu inda yace idan suka ci gaba da haka nan bada jimawa ba zasu zama sojojin sama mafiya karfi a Africa

Drop Your Comment

0 Comments