Kada wata musulma ta sake ta dau ciki -Gwamnatin China ga yan kasar ta - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Kada wata musulma ta sake ta dau ciki -Gwamnatin China ga yan kasar ta

Gwamnatin kasar china tayi gargadi da kuma yin kashedi kan cewa kada wata musulma ta sake ta dau ciki, muddun haka ya faru abun da zai biyo baya bazai yi dadi ba.

China na daukar tsauraran matakan tilasta wa ‘yan kabilar Uighur da wasu tsiraru rage haihuwa da zummar dakile yawan al’ummar Musulmi, yayin da a gefe guda, gwamnatin kasar ke karfafa wa ‘yan kabilar Han guiwar ci gaba da haihuwa.

A can baya, daidaikun mata sun yi korafi game da tilasta musu takaita haihuwa, kuma wannan tilastawar ta dada tsananta a yanzu kamar yadda binciken Kamfanin Dillancin Labaran AP ya nuna.

Wannan tilastawa da ake nuna wa kamar nuni ne  ga cewa ana so ne a rage yawan musulman kasar duba ga musulman kasar na dada yawa a fadin jihohin dake dukkan kasar.


To ko shin dokar da kasar china din tasa zaiyi tasiri ganin ba yanzu ne kasar take sa irin wa'innan dokokin ba musamman in aka yi la'akari da kasar tana da karfin tattalin arziki da zata iya ciyar da yan kasar ta, ammma take kokarin tilasta musu barin haihuwa.

Drop Your Comment

0 Comments