Babu wanda ya hallakar da kasar nan kamar Buhari - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Babu wanda ya hallakar da kasar nan kamar Buhari

Zaman Buhari Shugaba a kasar nan babbar musiba ce da jarrabawa ga Nigeria da mutanen cikinta, tarihi ya hakkake cewa ba'a taba shugaban da ya lalata kasar nan ya kawo yunwa, tsadar rayuwa, kashe-kashe da rashin tsaro irinsa ba, ba'a taba samun asarar rayuka kamar lokacinsa ba, saboda tsabar kisan da 'yan ta'adda ke wa sojoji yau sojoji ne  ke guduwa suna barin aiki, wani shahararren masoyin Buhari a nan Facebook ya tabbatar cewa fiye da soji dubu goma suka ajiye aikin soja a mulkin Buhari.

A matsayinsa na shugaba ba ya wani kokari don dakile zubar da jini da ake wa al'umma yana can fadarsa yana kodumo kayansa, anyi -anyi ya dauki matakin dakile wannan matsala ta hanyar garambawul ga manyan hafsoshin tsaro yaki yayi don ba zuri'arsa ake kashewa ba, kwanaki ya fito yana gargadin hafsoshi cewa wannan itace damarsu ta karshe, amma daga lokacin kawo yanzu babu abinda ya canza, don kullum sai an shekar da jinin al'umma, amma saboda rashin imani da tausayi da rashin damuwa da rayuka yayi burus yaki ya aikata komai, a karkashin mulkinsa 'yan ta'adda sun kashe sojojin Nigeria dubunnai ba'a dauki mataki ba, amma soji dari aka kashe a kasar nijar sai da aka cire shugabannin tsaro, kuma haka ba karamin tasiri yayi, duk da abinda ke faruwa saboda fitsara da rashin kunya sai ka sami wani ya fito yana yabon Buhari ya ayyana shi a matsayin mutumin kirki koh? Ai shike nan Allah na madakata, wallahi ba zamu taba yafe wa Buhari ba.

Babu lallai ba dole a cikin mu'amala, in kalamaina ba sa maka dadi kayi blocking dina kawai, kamar yadda ba zan taba barin wani ya fada min maganganun banza a kasan rubutuna ba tare da nayi blocking dinsa ba. Ko waye wallahi.

Daga: Indabawa Aliyu Imam

Drop Your Comment

0 Comments