Za'bada 5 million ga duk Wanda Yakawo shi a mace ko a raye - Gwamnati Katsina - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Za'bada 5 million ga duk Wanda Yakawo shi a mace ko a raye - Gwamnati Katsina
Da dumi-dumi: Wake Son Kudi?

Rundunar Yan sandan Jihar Katsina, tace zata Bayar da ladar Naira Milyan Biyar 5,000,000.00 ga duk Wanda ya bada bayani akan yadda za'a kama Adamu Aliero ko kuma ya kawo masu gawar sa.

Aliero wanda shine jagoran wadanda suka kai hari a garin Kadisau na Karamar hukumar Faskari ta Jihar, harin da yayi sanadiyyar kashe sama da mutane 20.
Adamu Aliero Dan Asalin Kauyen Yan kuzo ne na Karamar hukumar Tsafen jihar Zamfara, kuma ya hada kai da manyan Yan ta'adda ne domin kai hari a kauyen Kadisau.

Kamar yadda Kwamishinan Yan sandan Jihar ya bayyana, yace Bayanai sun nuna cewar Aliero ya kitsa kai harin ne saboda Yan sanda suna rike da Dan sa mai suna Suleiman Kamar yadda zakuga hoton Adamu Aliero a nan Kasa.

To al'umma sai a bazama neman wannan gawurtaccen Dan ta'adda Adamu Aliero domin kawo shi a mace ko a raye domin samun wannan babbar lada ta Naira Milyan Biyar 5,000,000.00

Drop Your Comment

0 Comments