Yadda Ake Tilasta Mini Yin Lalata Da Namiji Ina Jinin Al'ada - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Yadda Ake Tilasta Mini Yin Lalata Da Namiji Ina Jinin Al'ada

Mimidoo yarinya ce ƴar shekara 18 kuma ƴar asalin jihar Benue, makwabciyarta ta yaudare ta inda ta kai ta Burkina Faso domin yin karuwanci.
Mimidoo ta ga abubuwan mamaki tun a farko lokacin da mai riƙonta ta tilasta mata kwanciya da wani kan kudi 50,000 na CFA duk da tana jinin al'ada.
Abin ya zo wa Mimidoo kamar wasan kwaiwayo duk da ta ce a'a, amma uwar gidan ta yi wa rayuwarta barazana inda ta tilasta mata yin karuwancin.
BBC ta ziyarci inda take farfadowa kuma ake kula da da ita a Abuja bayan halin da ta shiga.
"Na ce mata ba zan yi karuwanci ba, amma ta ce za ta duke ni har sai na mutu idan ban yi ba. Saboda tsoro, haka na haƙura na fara wannan karuwancin," in ji Mimidoo .
Tun a lokacin, Mimidoo ta fara yin karuwanci domin tara kuɗin da suka kai sama da miliyan biyu na CFR domin sayen ƴancinta.
Tafiyar yini uku
Mimidoo tana zaune lafiya tare da iyayenta masu karamin karfi, kwatsam sai makwafciyarta ta ce mata tana neman ƴar aiki da za ta kai Burkina Faso.
Sai Mimidoo ta ji daɗi inda ta amince cikin sauri, amma da ta faɗa wa mahaifiyarta, sai ta hana ta.
Wadda za ta kai Mimidoo ƙasar ta shaida mata cewa ƙasar ba ta da nisa, ba ta wuce zuwa Ibadan ba, amma sun shafe kwanaki uku suna tafiya.
Amma a lokacin da ta isa, a nan ne ta san cewa ta zo yin karuwanci ne, kuma za ta rinƙa nemo kuɗi a kullum domin sayen ƴancinta.
"A kullum, ina kwanciya da maza bakwai domin tabbatar da cewa na samu kuɗin da zan biya uwargida ta."
Sana'ar karuwanci bayan zubar da ciki
Wani ɗan Burkina Faso ya fi son ya yi kwanciya da macen da ke jinin al'ada ba tare kororon roba ba, kuma Mimidoo, tana nan.Bayan ta gwada na farko, sai rashin lafiya ta kama ta har ta kasa ci gaba da rayuwarta ta yau da kullum.
Uwar gidanta ta bata wani abu ta sha, amma ba ta ji sauƙi ba har sai da aka fahimci cewa ashe juna biyu ne.
A Burkina Faso laifi ne a zubar da ciki, don haka uwar gidanta ta yi ƙokarin wata hanyar da za a zubar da cikin bayan ya gagara.
Ta sha wahala sosai amma daga baya an zubar da cikin - amma bayan kwana uku, uwar gidanta ta sake tilasta mata fita saman titi don ci gaba da samo mata kuɗaɗenta.
Yadda matsalar tsaro a Benue ke taimakawa safarar mutane
Kamar Mimidoo, masu safarar mutane na far autar ƴan mata suna sa su aikin karuwanci a ciki da wajen Najeriya.
Tun shekaru 12 zuwa 13 harakar safarar mutane ke bunƙasa kuma yanayin tsaro a Benue ke taimakawa harakar, a cewar Nathaniel Awuapila shugaban wata ƙungiyar sa-kai.
Rikicin Fulani da makiyaya da aka daɗe ana fama a jihar Benue, ya jefa mata da ƙananan ƴan mata cikin hatsari.
Mista Nathaniel Awuapila shugaban wata ƙungiyar ƙirkira da bincike da ake kira CORAFID ya ce matsalar ta fi shafar ƙananan hukumomi kamar Gwer-west da Agatu Ado da Guma da Logo da Oju da Gboko da
Ya ce wani lokaci masu safarar mutanen har auren ƴan matan suke yi ko kuma su shaida wa iyayensu cewa za su sa su makaranta, kuma a cewarsa akwai rauni ga matakan kariya a jihar wanda masu safarar ke amfani da damar.

Drop Your Comment

0 Comments