Tofa: Anata Cece kuce Gameda karbo Bashi Da Buhari keyi - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Tofa: Anata Cece kuce Gameda karbo Bashi Da Buhari keyiYunƙurin da gwamnatin Buhari ke yi na karɓar rance a gida da wajen Najeriya domin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2020 ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.
A ranar Talata ne majalisar dokokin Najeriya ta amince da buƙatar da shugaban ya aika mata ta karɓar rancen fiye da dala biliyon biyar bayan a watan Afrilu majalisar ta amince ya karɓo rancen naira biliyan 850 daga cikin gida.
Gwamnatin APC ta shugaba Buhari ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen da za ta karɓo rancen biliyoyin daloli ne domin cike gibin kasafin kuɗin musamman yadda annobar korona ta katse mata hanzari da kuma ƙalubalen da Najeriyar ke fuskanta ta fuskar kudin-shiga, sakamakon faɗuwar farashin mai a kasuwannin duniya.
Amma babbar jam`iyyar adawar kasar da wasu masana na sukar yawan rancen na shugaban wanda suke cewa yana tattare da hatsari ga makomar ƙasar.
PDP ta yi zargin cewa bashin da gwamnatin APC ke ci ya wuce kima - zai iya jefa Najeriya cikin wahala, kamar yadda Mista Kola Olabongdiyan sakataren yaɗa labaran jam`iyyar ya shaida wa BBC.
"Ƴunkurin Buhari na sake karɓar bashin sama da dala biliyan biyar, bayan sama da dala biliyon 22 da miliyon 79 da ya yi niyyar karɓa da farko don aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2020 ba tare da wani ƙwaƙƙwaran shirin biyan bashin ba, zai rage ƙimar kasarmu," in ji shi.
Mista Olabongdiyan ya kara da cewa yawan bashin da Najeriya ke karba zai buɗe ƙafa ga hukumomin da ke ba da rance na ƙasashen waje su mamaye bangarorin tattalin arzikin ƙasar.
Jam`iyyar PDP dai na fargabar cewa gwamnatin APC na ƙoƙarin jefa Najeriya cikin halin tsaka-mai-wuya ta hanyar mayar da ƙasar tamkar baiwa irin ta zamani, kasancewar ta sarayar da makomar ƴan Najeriya, ta yadda wasu hukumomin ƙasashen waje za su kafa musu ƙahon-zuƙa!"

Drop Your Comment

0 Comments