Sati biyu muka bayar kawai a canza su Buratai - Kungiyyar arewa - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Sati biyu muka bayar kawai a canza su Buratai - Kungiyyar arewa


Shugaban kasar Nigeria Muhammad buhari ya samu sanarwan cewar cikin sati biyu kawai aka bashi kan ya sanja su buratai in ji kungiyar gamayyar matasan arewa,  

A yayin da kashe - kashe rayuka da asarar rayuka suka cigaba da faruwa a arewacin Najeriya, gamayyar kungiyoyin kishin arewacin Najeriya sun bawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wa'adin kwanaki 14 ya sauya dukkan shugabannin rundunonin tsaro.

Kungiyyar ta kuma karawa da cew bataga amfanin da jami'an tsaron Nigeria suke yi ba da har ya zuwa yanzu baza aga canji a harkan tsaron kasar ba kullum rayukan jama'a sai salwanta sukeyi,  kuma abun kaico ma mafiya yawan masu mukaman gwamnatin yan arewa ne a yanzu, 

A wani labarin kuma kungiyyar ta sanar da fara yin zanga-zangar ta a duk fadin jihohin nan dan nuna takaicin su da ko inkula da ake nunawa rayukan yan kasa a wannan mulkin. 

Drop Your Comment

0 Comments