Murna Ta koma Ciki a Garin Lagos Daga Musulmi har Christian - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Murna Ta koma Ciki a Garin Lagos Daga Musulmi har Christian


Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriyata ta ce ta dage lokacin da za a bude majami'u da masallatai har zuwa wani lokaci a nan gaba.
Gwamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu ya ce an yanke hukuncin hakan ne sakamakon yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar korona a jihar.
A baya dai gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar bude masallatai da majami'u a ranakun 19 da 21 na wanann wata.
A wani taron manema labarai da gwamnan ya yi ya nuna matakin dakatar da budewar wuraren ibadun nan take na da nasaba da yadda ake kara samun karuwar wadanda ke harbuwa da cutar coronavirus a jihar.
Ya ce a yanayi irin wanann da cutar ke karuwa bude wuraren ibadar na iya jefa al'umma cikin hadari.
"Ina sanar da ku cewa ba za mu ci gaba da bude wuraren ibada kamar yadda mu ka fada tun farko ba. Ba za mu bude wuraren ibada a ranar 19 da kuma ranar 21 ba. An dakatar da bude su har sai abin da hali ya yi.
"Dole ne mu sake nazari mai zurfi game da halin da muke ciki kan cutar COVID-19 a matsayinmu na jiha. Nazarin da muka yi ya nuna ma na bukatar da a dage lokacin bude masallatai da majami'u a jihar. Ba za a bude wuraren ibada a karshen makon nan ba," in ji gwamnan.
A makon da ya gabata dai gwamnan jihar Legas yac e ce za a bude masallatai a ranar 19 ga watan nan na Yuni, a yayin da kuma za a bude majami'u na mabiya addinin kirista a ranar 21 na wannan wata.
Tun kafin wannan sanarwa gwamnatin jihar Legas ta nuna rashin jin dadinta a game da yadda al'ummar jihar ke nuna halin ko in kula game da kiyaye kan sharuddan mu'amala a cikin al'umma a wannan yanayi da ake ciki na cutar korona.
Tuni dai jama'ar jihar suka fara tofa albarkacin bakinsu game da yadda gwamnatin jihar Legas ta yi amai kuma ta lashe game da dage lokacin bude wuraren ibada a jihar.
Da yawa daga al'ummar jihar Legas dai a 'yan makwanin nan da wuya akan samu mafi yawa daga mazauna jihar da ke sanya kyallen rufe fuska ko kuma samar da tazara walau a kasuwa ko taro.
Ko a makwannin baya jami'an 'yan sanda a jihar sun rufe wasu otel-otel da suka bude ana sharholiya a yayin da cutar take tsakiyar tayar da hankali.
Gwamnatin jihar ta jaddada dakatarwa wanda ta hada da wuraren shakatawa da tarurruka da kulob-kulob a fadin jihar.
Rahotanni na baya-baya sun nuna cewa jihar Legas tana da adadin mutum 7,319 da aka tabbatar da sun kamu da Covid-19.
A cikin wannan adadi, 1,137 sun murmure kuma an sallame su, yayin da 82 suka mutu, sun bar adadin 6,100 na zaune a ƙarƙashin kulawa.
Jihar Legas dai ita ce a kan gaba da yawan wadanda suka harbu da cutar a lokacin da adadin wadanda suka harbu a fadin Najeriya ya haura mutum 16,000.

Drop Your Comment

0 Comments