Muna Ciyar da Yara suna Gidajen Iyayensu - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Muna Ciyar da Yara suna Gidajen Iyayensu


Minista Sadiya umar tace za'a ci gaba da ciyar da dalibai abinci har zuwa gidajen su,  bullowar cutar nan bazai hana abun ya tsaya ba, wanda hakan ba karamin taimakawa zaiyi ga magidanta masu karamin karfi ba, 

inda tuni sanarwan ya tabbatar har anfara rabar da abincin a wasu yankuna na sassan kasar nan a yanzu haka.

Punch ta ruwaito an kaddamar da ciyarwar ne a wata makarantar firamri dake garin Kuje a babban birnin tarayya Abuja, Central Science Primary School.

Ministar kula da bala’o’i da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouk ce ta kaddamar da aikin, inda tace gwamnati na kashe daruruwan miliyoyi a duk rana don ciyar da daliban.

Ba karamin aiki bane, kuma yana lakume manyan kudi saboda burinmu mu isar da abincin ga gidaje miliyan 3.1 a duk fadin Najeriya. Amma ba zan fada maka tabbataccen kudin da muke kashewa ba.” Inji ta.

Ministar ta ce tsarin mai suna National Home-Grown School Feeding Programme yana samun kudin kashewa ne daga gwamnatin tarayya, amma gwamnatocin jahohi ke gudanar da shi.

Ministar ta ce ma’aikatar tare da hadin gwiwar gwamnatocin jahohi sun samar da tsarin kai abinci zuwa gidajen yaran da ke cin gajiyar ciyarwar a makarantu don cimma wannan manufa.

Ana saran ciyarwan zaici gaba da gudana har ya zuwa komawar yaran makaranta inda zasu ci gaba da karatu.

Drop Your Comment

0 Comments