TALLAFIN RUWAN LEDA (PURE WATER) DAGA MATAR GWAMNAN BAUCHI.

Uwar gidan gwamnan Jihar Bauchi ta bada tallafin abun sana'a da dogaro dakai wa mata a jihar Bauchi. Yayin da take gabatar da tallafin, mai dakin gwamnan ta hore wadanda suka amfana da tallafin ruwan cewa su alkinta abinda aka basu kada suyi almubazzaranchi dashi.

A yayin gabatar da jawabin godiya, daya daga chikin matan da suka amfana da tallafin tayi godiya da fatan Allah ya biya da gidan aljannah a madadin sauran.