Maharan Bindiga sun yi kisa mafi muni a Zamfafa - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Maharan Bindiga sun yi kisa mafi muni a Zamfafa


Wasu mahara da ba'a san suba sunyi wa mutanen kauyen kadisau ta jihar katsina mummunar barna,  jama'ar garin sun shaida zuwan maharan,  isowar su ke da wuya suka hau harbi ba babba babu yaro, sun kashe mutane fiye da 30 yayin da ake kan duba sauran gawarwakin jama'an da ba'a gani ba. 

Wani Mazaunin garin na Kadisau ya shaida maba ta waya cewa “maharan sun zo ne da yammacin jiya talata da Misalin karfe biyar, suka fara harbe-harben kan mai uwa-da-wabi a garin. Mutane su kai ta gudun neman tsira, sun kwashe sama da awa ukku suna cin karensu babu babbaka a garin ba tare da Jami’an tsaro sun kawo mana dauki ba, duk da kokarin da muka yi na sanar da su.

A gefe guda mazauna Nigeria suna Allah wadai da wannan sakacin na gwamnati,  la'akari da kullum ana kashe fararen hula batare da ankawo karshen zubda jinin da akeyi ba. 

Drop Your Comment

0 Comments