Kunsan dalili: Gwamnatin Nigeria ta baiwa Kasar China Dala Miliyan $318 - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Kunsan dalili: Gwamnatin Nigeria ta baiwa Kasar China Dala Miliyan $318


Jama'ar Nigeria sun fara kaico da kudin da Kasar Nigeria ta baiwa kasar Sin na har Kimanin Dala $318, hakan na faruwa ne biyo bayan Halin matsalar rashin tsaro da kasar take ciki a yanzu haka inba'a manta ba tun kwanakin baya tsaro ya sursurce a kasar.


Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da biyan Dalar Amurka miliyan dari uku da goma sha takwas ($318m) ga Gwamnatin Kasar Sin (China) akan aikin hanyar jirgin kasa wacce ta tashi daga Ibadan zuwa Kano

Haka kuma Ministan sufuri na Najeriya wato Mista Rotimi Amaechi ya sanar da cewar aikin layin dogon na bangaren Legas zuwa Kano shima za'a fara shi a karshen watan Ogusta mai zuwa inda aikin zai faro daga Kano.

Sai dai wasu suna ganin da wainnan kudaden da kamata yayi  gwamnati tasayi makamai ta bawa jami'ai don kafe kansu da kasar daga halin da ta tsinci kanta. Wannan hali na matsalar tsaro na dada dagawa jama'ar kasar hankali ganin kullun a cikin firgici da zaman makoki suke.

Drop Your Comment

0 Comments