Kudancin Nigeria sun fi kowa Morar Mulkin Buhari Da Mukamai - Harsashe - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Kudancin Nigeria sun fi kowa Morar Mulkin Buhari Da Mukamai - Harsashe


Bayanan da wani babban jami'in gwamnatin Muhammadu Buhari ya wallafa sun nuna cewa yankin Kudancin kasar ya fi samun mukamai a gwamnatinsa idan aka kwatanta da Arewacin kasar.
Bashir Ahmad, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan shafukan zumunta, ya wallafa wasu alkaluma ranar Talata wadanda suka nuna cewa Kudancin Najeriya ya samu kashi 54.2 na mukaman da Shugaba Buhari ya raba tun da ya hau kan mulkin a shekarar 2015 zuwa watan Mayun 2020.
Arewacin kasar ya samu kashi 45.8 daga cikin dukkan mukaman da shugaban kasar ya raba.


Alkaluman sun nuna cewa a ciki wadannan yankuna, Kudu Maso Yamma, wato yankin Yarbawa inda mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, ya samu kashi mafi tsoka na mukamai a gwamnatin Buhari.
Yankin na Yarbawa ya samu 33.7 na mukaman da Shugaba Buhari ya nada.
Yankin Arewa Maso Yamma, inda Shugaban kasar ya fito shi ne na biyu rabon mukamai a gwamnatin ta Buhari inda ya samu kashi 19.5

Sai kuma Arewa Maso Gabas mai fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, inda kusan daukacin hafsoshin tsaron kasar suka fito, wanda ya samu kashi 15.3.
Kudu Maso Gabashin Najeriya inda 'yan kabilar Igbo suka fi yawa shi ne kurar-baya a rabon mukaman da Shugaba Buhari ya yi inda ya samu kashi 7.9.
Da ma dai yankin ya dade yana korafin cewa an bar shi a baya wajen rabon mukamai a gwamnatin Shugaba Buhari, ko da yake galibin mazauna yankin sun ki zabar jam'iyyar APC mai mulki inda suka zabi jam'iyyar hamayya ta PDP.

Drop Your Comment

0 Comments