Koriya ta buƙaci Amurka ta fita harkarta idan tana son gudanar da zaɓe lafiya - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Koriya ta buƙaci Amurka ta fita harkarta idan tana son gudanar da zaɓe lafiya

Koriya Ta Arewa ta bukaci Amurka ta tsame kanta daga harkokin kasashen Koriya biyu matukar Amurkan na son zaben shugaban kasarta da za a yi bana ya tafi yadda ya kamata.
Lamarin na zuwa ne bayan Amurkar ta ce ba ta ji dadin yadda Koriya Ta Arewa ta dakatar da hanyoyin sadarwa da Koriya Ta Kudu ba.
Wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewan KCNA ya fitar ta ce ya kamata Amurka ta yi gum tare da mayar da hankali kan magance matsalolinta na gida, idan dai ba so take ta gamu da abin da zai daga mata hankali ba.

Har yanzu ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba game da kawo karshen shirin Nukiliyar Koriya Ta Arewa duk da taruka masu dumbin tarihi da aka gudanar tsakanin Kim Jong-un da Donald Trump, sannan Koriya Ta Kudu na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda Amurka ta ki sassauta takunkuman.
A ranar Talata ne Koriya Ta Arewa ta ce za ta katse duk layukan sadarwa na hukuma da Koriya Ta Kudu ciki har da wani layin kiran gaggawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.
Mahukuntan birnin Pyongyang sun ce wannan ne na farko a jerin matakan da za su ɗauka kan gwamnatin birnin Seoul da suka bayyana da "abokiyar gaba".
Umarnin ya zo ne daga Kim Yo-Jong 'yar uwar Shugaba Kim Jong Un.
Matakin ga alama wani martani ne ga wasu takardun nuna adawa da gwamnati, da 'yan Koriya Ta Arewa da suka sauya sheƙa bayan sun tsere zuwa kudanci suka riƙa jefawa ƙasar ta sama.

Drop Your Comment

0 Comments