Ko Kun San Ma’aikaciyar Bankin Da Ta Yi Lalata Da Samari 200? - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ko Kun San Ma’aikaciyar Bankin Da Ta Yi Lalata Da Samari 200?


Ko Kun San Ma’aikaciyar Bankin Da Ta Yi Lalata Da Samari 200?
Wata ma’aikaciyar Banki mai kimanin shekara 39 ta shiga tasku bayan da aka same ta da laifin yin lalata da samari sama da guda 200 masu neman aiki, inda kowanne ta yi masa alkawarin daukarsa aiki.
Matar wacce aka bayyana sunanta da Mutale Winifridah, ita ce manajan reshen bankin ZANACO na kasar Zambia
Sama da samari goma ne suka shigar da kara akan yadda Winifridah mai shekara 39 ta yi ta amfani da su wajen biya mata bukatarta, dalilin da ya sa hukumomi a bankin suka fara bincike akanta, kuma daga karshe aka samu cewa ta dade tana amfani da damarta akan masu neman aiki da ma wasu maza masu mu’amala da bankin na ZANACO.
Wasu daga cikin mazajen sun koka kan yadda Winifridah ta ci gaba da yin amfani da damarta a matsayinta na manaja tana jin dadinsu bisa alkawarin za ta basu aiki ko kuma za ta taimaka musu da bashin banki.
Winifridah dai ta yi jinkirin yin aure ne sakamakon burin da ta ke da shi na cimma wani mataki na mallakar shaidar digirori a fannoni daban-daban kafin ta yi aure.

Drop Your Comment

0 Comments