Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nuna takaicin sa na yadda Yan ta'addan Boko haram suka Kai muggan hare-hare jiya har suka kashe kusan mutane 70 tare da kone-kone hade da satar shanu,  kamar yadda jaridar the cable ta rawaito. 

Kana shugaban kasar yayi kakkausar kira ga dakarun sojin kasar nan da kada su saurarawa 'yan Boko Haram. Ya ce su fanshe rayukan jama'arsa da aka kashe a kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar Gubio da ke jihar Borno.

Wannan abun takaici ne musamman yanzu da ake gaf da karatowar lokacin Bikin dimukuradiyya,  Shugaban ya fitar da jimamin sanne ta hannun mai magana da bakin sa Wato Garba Shehu.