Jihar kaduna ba Abuja bace nike da iko da jaha ta- elrufai - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Jihar kaduna ba Abuja bace nike da iko da jaha ta- elrufai

Gwamnan jahar kaduna malam Nasir Elrufai har yanzu bai aminta da bude ilahirin jahar kaduna ba, inda yake maidawa masu sukar sa da martani mai zafi. 

 Gwamnan na kaduna ya bayyana jahar kaduna dai jahar sa ce dan haka shi zai tafiya da mulkin jahar yadda yake so. al'ummar jahar ta kaduna dai suna bukatar a bude musu kasuwanni, guraren ibadu, saboda su samu damar ibada da kuma kasuwancin su. 

Kamar yadda sahohin yada labarai suka rawaito gwamnan ya bayyana;
"Jihar Kaduna ba Abuja bace. Don haka nike da iko da jiha ta, maganar Na janye doka baki daya bazan janye ba a halin yanzu."

Wannan martanin gwamnan Kaduna Nasir el-rufa'i ne yayi ne ga gwamnatin tarayyar Najeriya.  

Drop Your Comment

0 Comments