Ina Kudin da Ake warewa dan Yaki da Yan ta'adda - Gudaji Kazaure - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ina Kudin da Ake warewa dan Yaki da Yan ta'adda - Gudaji Kazaure


Gudaji kazaure ya bayyana abun kunya ne ace gwamnati tayi sulhu da yan ta'adda musamman tsagerun boko haram,  inda ya bayyana ina kudaden da ake warewa na sayan makamai, da kuma Tsaurara tsaron da akeyi yace bai kamata boko haram ta kai zuwa yanzu ba. 

Gudaji ya ya bayyana;
 “Ina kudin da aka ware wa bangaren siyan makamai? Ina Helikwaftar da ake da su? Me sojojin sama ke yi? ‘Yan bindigar nan na zuwa da rana tsaka akan baburansu fiye da su 200, tsaf za a iya kai musu hari ta jirgin sama cikin minti. Ina jami’an leken asiri? Abin kunya ne ga jami’an tsaron kasarnan a ce ana sulhu da ‘yan ta’adda, Inji Shi. 

Har yanzu kasar nan tana cikin fargaba da  fama da matsalar rashin tsaro duk da gwamnati na kokarin shawo kan matsalar, amma yan kasar suna dada ci gaba da ganin gazawar gwamnati a wannan fannin.

Drop Your Comment

0 Comments