Buhari ne ya jefa Arewa halin da take ciki - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Buhari ne ya jefa Arewa halin da take ciki

Manyan Dattawan Nigeria suna ci gaba da nuna takaicin su na yadda bubari yake nuna ko in kula da halin da yankin arewa take ciki, Duba da yanayin rashin zaman lafiyar yankin yakici yaki cinyewa kullum ana gwammatar jiya da yau hakan ya sa:

Kungiyar dattijan arewa (NEF) ta koka a kan halin rashin tsaro da arewa ke ciki tare da zargin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gaza yin maganin matsalar.

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Lahadi, jagoran kungiyar, Ango Abdullahi, ya ce lamari rashin tsaro ya na kara tabarbarewa a kullum.

Ya ce yawaitar hare - haren 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa alama ce da ke nuna cewa gwamnatin Buhari "ta fadi kasa warwas" a bangaren tsaro da walwalar 'yan kasa.

Kowa yasan tun hawan Buhari a mulki ake tsammanin zai kawo sauyi sai ga akasin haka mudaj bamuyi tsammanin haka ba daga gare ka. Wannan ba karamin ci baya akayi ba musamman Ace shugaban kasa dan arewa ne sannan yabar yankin sa babu tsaro.

"A bayyane take cewa gwamnatin Buhari da gwamnatocin jihohi sun rasa yadda zasu bullowa lamarin, sun gaza kare rantsuwar da suka yi a kan cewa zasu kare jama'a da dukiyoyinsu.


Drop Your Comment

0 Comments