Ana zargin Shugaba Buhari da sace Triliyoyin Naira - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ana zargin Shugaba Buhari da sace Triliyoyin Naira

Wata sanarwa da sakataren yada labaran Jam’iyyar Mr Kola Ologbondiyan ya fitar a karshen mako ta yi zargin cewa, tsoron bankado badakalar satar tarin kudaden ne ya tilastawa Muhammadu Buhari neman sake ci gaba da wanzuwa a mulki zuwa shekaru 4 masu zuwa.


Jam'iyar PdP kuma ta kara yin zargin kudaden da aka kwato daga hannun wasu shuwagabannin kasar nan har ya zuwa yanzu ba'ayi amfani da su ba,  kuma kudaden an rasa sama sukayi ko kasa.
Ka zalika sakataren jam’iyyar ta PDP Mr Kola Ologbondiyan ya kuma yi ikirarin cewa adadin kudin da Najeriya ta ciwo bashi shi ne mafi muni a tarihi, inda yanzu haka ake bin gwamnatin Buharin bashi Naira tiriliyan 24 da biliyan dari 3 da tara.

Wannan abu dai  ya bar baya da kura inda jama'a da dama suke sa ido domin ganin ko Gwamnatin tarayya zata fiddo da sauran kudin domin yiwa talakawa aiki. Saidai har ya zuwa yanzu shiru.

Drop Your Comment

0 Comments