Alamu na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da tsagin Victor Giadom a matsayin shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya - Hakan ta bayyana ne bayan Giadom ya samu sahalewar shugaba Buhari domin kiran taron ma su ruwa da tsaki a gudanar da harkokin jam'iyyar APC (NEC) - An tsayar da ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, domin gudanar da taron NEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja Tsagin shugabancin jam'iyyar APC da ke karkashin Mista Victor Giadom ya kira taron masu ruwa da tsaki a gudanar da harkokin jam'iyyar APC (NEC).