Bazan Kara Aure Ba - Inji Ali Nuhu - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Bazan Kara Aure Ba - Inji Ali Nuhu

Fitaccen jarumi kuma darakta a Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana cewa ba ya da burin kara aure, domin matarsa daya Maimuna Ali Nuhu ta ishe shi.

Ali Nuhu ya kara da cewa ba ya ga burinsa na zama da matarsa ita kadai, yana da burin ya haifi ’ya’ya hudu, duk da cewa ya ce Allah ne kadai Masani.

Ali Nuhu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC, inda ya ce, “Burina ina auri mace daya kawai. Maimuna Ali Nuhu.”

Jarumin ya kara da cewa, duk da cewa ba a cika ganinsa da Darakta Hafiz Bello ba, shi ne babban na hannun damansa domin sun taso tare kuma tun suna kanana har yanzu da suke tare a Manasa’antar Kannywood, ba su taba samun rashin jituwa ba.

Da aka tambaye shi tsakanin darakta da zama jarumi wanne ya fi so, sai ya ce, “Na fi son zama jarumi gaskiya.”

Sarki Ali Nuhu ya kara da cewa ba ya ga harkar fim da yake yi, yana kasuwancin kayan sawa da kiwon kaji.

Sannan ya ce ba ya zaton zai iya barin Kano domin ko da me ka zo an fi ka, “Don haka matukar ina raye ba na tunanin zan iya zama a wani waje bayan Kano domin kusan duk rayuwata a Kano na yi,”  inji shi.

Sannan jarumin ya kara da cewa yana kewar Borno saboda yana tuna lokacin idan sun je wajen kakarsu yadda take yi musu, “Wannan shi ne abin da ba na mantawa,” inji shi.

Game da batun ko yana da girman kai, Ali Nuhu wannan tambayar ce ya fi amsawa a rayuwarsa, inda a kullum yake bayar da amsa  cewa, “Mutum ya bari sai ya yi mu’amala da ni kafin ya gane ko ina da girman kai.”

“Sannan ina da baiwar waka a boye. Farkon shigowa ta Kannywood na yi waka mai taken fahimtar juna. Amma daga baya na bar waka saboda kada abubuwa su yi yawa,” inji shi.

Game da batun ko yana da ’yan mata a Kanyywod, sai ya ce, “Ba ni da ’yan mata a Kannywodd, sai dai ’ya’ya, irin su Hadiza Gabon da Maryam Yahaya da sauransu.”

Kan yaya yake ganin rayuwa nan da shekara 10, sai ya ce yana ganin lokacin ya yi ritaya, “ina rayuwa tare da ’ya’yana, watakila na samu jika.”

Drop Your Comment

0 Comments