Bazan Iya Barin Shirin Fim Din Kannywood Ba - Hadiza Kabara - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Bazan Iya Barin Shirin Fim Din Kannywood Ba - Hadiza Kabara

FITACCIYAR jaruma Hadiza Muhammad Sani, wadda aka fi sani da Hadiza Kabara, ta bayyana cewa har yanzu ba ta yi bankwana da harkar fim ba.
 

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin zantawar da ta yi da mujallar Fim.
 
A hirar, Hadiza ta ce, "Ba zan ce na yi bankwana da harkar fim ba, saboda wannan harkar ita mu ka iya tun mu na yara; da ita mu ka buɗi ido, saboda haka babu yadda za a ce za mu iya bankwana da harkar.
 
"Kawai dai abin da zan ce shi ne a yanzu an samu sauyi idan ka kwatanta da yadda ake gudanar da harkar a shekarun baya. 
 
"An samu bambanci mai nisa, domin yanzu akwai ƙarancin aikin, ba kamar yadda ake yi a baya ba. 
 
"Don yanzu sai ka ga an daɗe ba a fita lokeshin ba, don haka yanzu harkar ta zama wata iri saboda yanayin kasuwa."
 
Tsohuwar jarumar, wadda ke zaune a garin Kano, ta ƙara da cewa, "Kuma a yanzu wani sauyin da aka samu kusan an daina yin fim na kasuwa, sai fim mai dogon zango wanda za a kalle shi a manyan gidajen talbijin.
 
"Don haka abin da zan iya cewa, harkar a yanzu ta zama sai addu'a!"
 
Wakilin mu ya tambaye ta cewa da yake yanzu ta na yin aikin ne da yara waɗanda da yawa ma ba ta san su ba, ko yaya ta ke ganin kan ta a cikin su?
 
Hadiza Kabara ta amsa: "Gaskiya ne abin da ka faɗa, baƙin fuska ne a waje na, amma duk da haka mu na zaman lafiya da su, su na ganin girma na, don haka lafiya mu ke yin aiki da su cikin girmamawa. 
 
"Kuma za ka ga ina fitowa a yayar su, wasu ma a uwar su na ke fitowa, don haka babu abin da ya ke haɗa mu da su sai alheri."
 
Dangane da yadda a can baya ta saba fitowa a fim a matsayin budurwa, ko yaya ta ke ji a yanzu da ta ke fitowa a matsayin uwa ko yaya?
 
Sai ta ce, "Ai lokaci ne, kuma Allah shi ya ke da zamani, don haka ba zai yiwu ba a ce a yanzu zan fito a matsayin budurwa ba saboda zamani ya sauya, don haka a yanzu dole ne na fito a matsayin uwa ko a yaya ko matar wa, da sauran su."
 
Da yake 'yan kwanakin nan aka fara ganin ta a fim ɗin 'Gidan Badamasi, mujallar Fim ta tambaye ta ko shi ne shirin ta farko da ta yi bayan ta dawo harkar.
 
Sai ta ce, "Gaskiya na yi wasu da dama, daga baya ne na yi 'Gidan Badamasi', wanda shi ne duniya ta fara sani na da shi a wannan lokacin kafin kuma daga baya na shiga cikin shirin 'Daɗin Kowa' na Arewa24 wanda na ke taka rol ɗin Lantana mai adashi, kuma har  Allah ya sa yanzu na saba da yadda ake gudanar da harkar ma.

Don haka duk yanzu mun zama ɗaya da sauran jaruman da ake yin aikin 'Daɗin Kowa' da su."
 
Hadiza Kabara ta yi godiya ga Allah da ya sa duk da tsawon lokacin da ta ɗauka ba ta yi fim ba, amma ta na dawowa sai ta ga masu kallo ba su manta da fuskar ta ba.
 
"A yanzu ma na ƙara samun ɗaukaka, don haka ina yin alfahari da wannan damar da na samu a wannan lokacin da na ga jama'a sun karɓe ni, su na so na kamar yadda su ka yi mini a baya," inji ta.

Daga: Fim Magazine

Drop Your Comment

0 Comments