Ali Nuhu Ya Wuce Matsayin Aboki Agurinah - Inji Nafisa Abdullahi - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ali Nuhu Ya Wuce Matsayin Aboki Agurinah - Inji Nafisa Abdullahi

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta yi karin haske game da matsayin Ali Nuhu a wajenta musamman ma dai a harkokin masana'antar.

Jarumar wacce ta ce ta fito a fina-finai da dama da ta kiyasta da 'sama da 50', ta shaida wa majiyar mu ta BBC a lokacin da ta zanta da ita kai tsaye a dandalin sadarwar zamani na Facebook cewa fitattcen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya wuce matsayin aboki a wajenta.

Sadikblog ta tsinkayi jarumar na cewa "Ba zan kira Ali Nuhu aboki ba, ya wuce matsayin aboki."

"Yadda zan zauna na yi magana da sauran jarumai, ba zan iya yi da Ali Nuhu ba," in ji Nafisa.

Ta ce Ali Nuhu ne sanadin fara zuwanta Kannywwod.

Nafisa Abdullahi dake zaman daya daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood ta kuma bayyana yadda ta soma shiga harkar fim bayan ta hadu da jarumi Ali Nuhu a shekarun baya a jihar Bauchi.

Drop Your Comment

0 Comments