Abinda Ya Kamata Kusani Game Da Kamfanin FKD Na Ali Nuhu - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Abinda Ya Kamata Kusani Game Da Kamfanin FKD Na Ali Nuhu

Shahararren kamfanin shirya Finafinan Hausa mai suna 'FKD Production' ya cika shekaru 20 da kafuwa a cikin watan da ya gabata.


Kamfanin wanda mallakin fitaccen jarumin Kannywood ne, wato Ali Nuhu. Ma'anar cikakken sunan kamfanin shi ne:

F: Fatima
K: Karderam
D: Digema

Ali Nuhu yayi amfani da sunan mahaifiyar sa wajen kirkirar sunan kamfanin.

Ba a banza ake kiran Ali da Sarkin Kannywood ba. Idan aka yi la'akari da dadewar sa a masana'anatar shirya Finafinan Hausa da kuma yadda ya mamaye harkar ta sigogi da dama, duk da yake akwai yawaitar jarumai amma har yanzu shi ne sama kamar sakaina a kan ruwa.

Kamfanin FKD ya sha bamban sauran kamfanoni da ke a Kannywood, mafi bambanci tsakanin sa da sauran kamfanoni shi ne ta yadda ya yi kokarin gina wasu jarumai, har su ma Allah ya sa aka samu damar damawa da su a masana'antar.

Allah ne mai daukaka bawan sa a duk lokacin da ya so. Amma Ali ya zama silar gina jarumai da dama a farfajiyar finafinan Hausa, da yawa daga cikin su a yanzu su ma suna cin gashin kan su.

A Yanzu ma akwai jarumai da ya saka a gaba don ganin su ma sun taso. Haka zalika, kamfanin FKD Productions, shi ne kamfani daya tilo da ya fi kowane kowane kamfani samun kyaututtukan karramawa a gida Nijeriya da kuma kasashen ketare. Inda har kirari ake yi wa mai kamfanin da "Multiple Awards Winning Actor"

Koda yake, kamfanin bai cika yin Finafinai barkatai ba, amma duk lokacin da FKD za su fitar da sabon fim din su, za a ga hankalin makallata Finafinan Hausa ya karkata a kan su, don ganin wace irin sabuwar waina da suka toya a cikin sa.

Kamfanin, ya tabo kusan kowane jigo, na rayuwar dan Adam, tun daga kan ''Zamantakewar Auren Hausawa' Illar Shaye-Shaye, Tauhidi, Zaman Amana, Rayuwar Matasa, Illar Shaye-Shaye, Illar Cin Amana, Amfanin Zumunci, da sauran su.

A cikin shekaru 20 da kafuwar kamfanin, sun shirya Finafinai za su kai akalla guda 34 a wanda su suka dauki nauyin su.

Fim din kamfanin na farko wanda suka fitar a kasuwa shi ne, "Sabani" an yi shi ne a watan Janairu 2000. Sai kuma fim din su karshen wanda suka fitar a kasuwa shi ne "Kar Ki Manta Da Ni" sai kuma sabo mai suna "Bana Bakwai" wanda shi ma yana kan hanya.

Daga : Kannywood Exclusive

Drop Your Comment

0 Comments