Ni Dai Na Bar Gaba Da Hadiza Gabon - Inji Nafisa Abdullahi - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ni Dai Na Bar Gaba Da Hadiza Gabon - Inji Nafisa Abdullahi

Babbar jarumar din Hausa, wato Nafisa Abdullahi, ta ce tana zama da kowace jaruma ce “A kan yadda take so su zauna tare.”Jaruma Nafisa, ta yi wannan bayanin  ne, a cikin wata hira da aka yi da ita kwanaki

Jarumar take cewa ,

“Duk wacce ke son mu zauna da ita lafiya lau, to za su zauna lafiya babu komai, wacce ita kuma ke da akasin haka to takan tafiyarta da ita ta yadda take so ayi”


Ta fada cewa ita yanzu a tsakaninta da ‘yan shirin fim, “Babu wadda ba sa zaman lafiya.”

Jarumar ta kara haske a kan zaman takewar ta da jaruma Hadiza Gabon, wadda suka samu matsala a kwanakin baya.

Ta ce Amma yanzu sun shirya a tsakanin su


Nafisa ta ce, rashin haduwa da jarumar sosai yasa ake mata tunanin suna gaba amma idan sun hadu suna gaisawa

Drop Your Comment

0 Comments