Mun yi auren mut'a da Isah A. Isah, inji Sadiya Haruna - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Mun yi auren mut'a da Isah A. Isah, inji Sadiya Haruna

Sadiya Haruna, matashiyar nan wadda ta yi kaurin suna wajen sayar da kayan mata da kuma yin bidiyo na batsa a dandalin sada zumunta na Instagram, ta yi ikirarin cewa ita da fitaccen jarumi Isah A. Isah sun taba yin auren mut'a na tsawon wata uku.


Haka kuma ta yi masa wasu zarge-zargen, ciki har da cewa wai shi dan luwadi ne.
Jarumar ta fadi haka ne a wani bidiyo da ta dauka ta tura a shafin ta na Instagram, wanda ya jawo ka-ce-na-ce a tsakanin mabiya soshiyal midiya.
Bullar bidiyon ya sa mutane da dama su ka yi tir da abin da su ka aikata, har wasu su ka rika yada shi a YouTube da taken "Yadda Ake Auren Mutu'a A Kannywood".
Amma dai Isah ya fito ya karyata zargin, inda ya yi rantsuwa da Allah cewa shi bai taba yin luwadi ba, kuma bai taba neman ta da zina ba.
Sadiya dai ta yi wannan bidiyo ne sakamakon wani bidiyo da Isahn ya yi inda ya ba jama'a hakuri bisa wani kuskure da ya ce ya tafka, wanda bai bayyana ko menene ba.
Bayan bullar bidiyon na Sadiya, sai Isah ya goge nasa daga Instagram. Daga nan sai ya kai ta kara wajen 'yan sanda, su kuma su ka gurfanar da ita a kotu bisa zargin bata suna, laifin da ya saba wa sashe na 391 na kundin Penal Code.
A ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2019 wata kotun majistare a Kano mai lamba 15 ta saurari karar, inda mai shari'a Muntari Garba Dandago ya karanto kunshin tuhumar da ake yi mata sannan ya bayyana cewar Isah A. Isah ne ya yi korafin cewar ta bata masa suna.
Sadiya ba ta amsa laifin ta ba.
Daga nan kotu ta tura ta gidan yari bayan ta dage sauraron karar.
A wani binciken diddigi da mujallar Fim ta yi, mun gano cewa Sadiya Haruna 'yar asalin Karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno ce, sannan 'yar kabilar Margi ce.
Wata majiya ta bayyana mana cewa ta taba yin aure har ma ta na da 'ya'ya 5, kuma bayan sun rabu da mijin ne ta koma Legas da zama, inda su ka kama haya a unguwar Ikorodu.
Sadiya ba ta dade sosai a masana'antar Kannywood ba, domin kuwa ta shigo harkar fim ne a cikin Nuwamba 2017 ta hanyar wani matashin furodusa dan asalin Jihar Katsina mai suna Nura Bilya ABB, mai kamfanin ABB Nigeria Limited da ke Legas.
An fara sanya ta a wani fim din Nura din mai suna "Bakon Lagos", wanda mujallar Fim ta ba ku labarin shirya shi a Ikko a fitowar ta ta Disamba 2017.
Amma tun daga wannan fim din, babu wanda ya kara sanya Sadiya a fim.
Sai dai a farkon shekarar 2018 jarumar ta dauki nauyin shirya fim nata na kan ta mai suna "Soyayyar Facebook" wanda aka dauke shi a Maiduguri, Jihar Borno. Amma har yanzu bai fito
kasuwa ba sakamakon cuta tare da zaluntar da ta yi zargin daraktan fim din ya yi mata.
Tun daga wurin aikin fim din ne rigimar ta ta farko a Kannywood ta faru, inda ta zargi shugaban kungiyar jaruman Kannywood, Alhassan Kwalle, da cewa ya neme ta da lalata, kuma ta ce saboda ba ta ba shi hadin kai ba ne ya gudu daga lokeshin din.
Alhassan ya fito ya kare kan sa a wani guntun bidiyo mai tsawon minti 6, wanda ya rika tura wa mutane ta WhatsApp. Sannan ya sa 'yan sanda su ka kulle Sadiya na tsawon kwana daya a Kano. A lokacin, an zargi Isah A. Isah da daure mata gindi tare da kokarin yin belin ta.
Bayan ta fito, sai ta yi bidiyo inda a ciki ta bayyana cewa ita ba 'yar Kannywood ba ce, sannan ta ba duk wani dan fim hakuri.
Daga nan darakta Sunusi Oscar 442 ya yi mata wasu bidiyoyi na wakokin yabon Manzon Allah (S.A.W.), wanda ya sa aka daina ganin maganganun batsa da ta ke yi tare da fiddo nonuwa da ta ke yi a wasu bidiyoyin da ta ke yadawa a Instagram.
Haka kuma ta goge duk wani bidiyo da ta yi wanda ya nuna tsiracin ta, kuma ta sauya sunan ta daga Sadeeya Haruna zuwa "Sayyada Sadeeya Haruna".
Su dai wakokin yabon Annabi wadanda ta yi maimun din su a bidiyo, mallakar mawaki Hafiz Abdallah ne.
Da yawan mutane sun fara tunanin kila wakokin ne sanadiyyar shiryuwar ta.
Kwatsam, ba a fi sati ba da tunanin tubar da ake ganin ta yi na daina shigar banza, sai aka ga ta yi wannnan bidiyo inda ta ragargaji Isah A. Isah tare da bugun gaban idan ya isa ya fito fili ya karyata ta.
Ya zuwa yanzu, Sadiya ta yi fada da 'yan fim akalla mutum 10. Ban da Alasan Kwalle da Isah A. Isah, wasu wadanda ta taba zagi a Instagram su ne: Hadizan Saima, Nasiru A. Dorayi, Teema Makamashi, Naja Ta Annabi, Misbahu M. Ahmad, Abba Daneji, Lawal Sa'idu Washasha, da Aminu Dagash.
Duk da irin cin kashin kajin da ake zargin Sadiya ta na yi wa 'yan Kannywood amma har yanzu akwai wadanda ke mu'amala da ita, wanda a ganin wasu duk wanda ta yi mu'amala da shi sai ta zage shi. A yanzu haka dai kowa ya bar kula ta in ban da Adam A. Zango da yaran sa.
Wasu masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce Zango ne mutum na gaba da ake jin Sadiyar za ta zaga in dai su ka ci gaba da tafiya tare.


Tuni dai jarumar ta fito daga gidan yari, ta na ci gaba da sharafin ta a soshiyal midiya. Ko da ba ka bibiyar ta, to kila wata ran ka ci karo da bidiyon ta

Drop Your Comment

1 Comments