Ba Laifi Bane Don Ali Nuhu Ya Kwaikwayi Fim Din Indiya - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Ba Laifi Bane Don Ali Nuhu Ya Kwaikwayi Fim Din Indiya

SHIGA SHARO BA SHANU.


Na ga wani rubutu da wata da mai suna Fadila H. Aliyu Kurfi ta yi game da jarumi Ali Nuhu da kuma Mahangarta a Finafinan Hausa wadda ta bayyana jarumin a daya daga cikin jaruman da ke so rushe masana'antar, na so na yi shiru bayan na ga tsokacin na ki, sai dai ya zama tabbas na nuna maki hanya Dodar sannan kuma na fito da ke daga cikin ramin da ki ka afka wanda na tabbata ba za ki iya fito da kan ki ba a cikin rijiyar mai gaba dubun da ki jefa kan ki a ciki ba.

Da farko dai zan fara da sanar da ke cewa shi fa labarin masana'antar Finafinan Hausa ya sha bamban da irin labarin su Gogaji da wargaji wanda ki ka fi kwarewa a kan sa, domin a tsokacin na ki ya nuna tabbas ke makauniya ce sannan kuma ba ki san abubuwan da ke faruwa a harkokin Finafinan Hausa ba, domin da ace sharhi ne ki ka yi game da tashin hodoji masu karawa mata haske ko tanka maki ba zan yi ba na tabbata kina da kwalin digiri a wannan bigiren.

Kafin na shiga gundarin abin da ki ka rubuta, zan so ki fahimci cewa ni ba yaron Ali Nuhu ba ne, hasalima ina daya daga cikin masu sukar sa tare da tunatar da shi a kan dukkan wasu abubuwan da ya ke yi a bisa kuskure wanda na ke da masaniya a kan su.

Kaco-kam kin daurawa Ali laifin soyayyar Finafinan indiya, ko shakka babu ga duk wanda ya san Ali Nuhu in dai ba sanin shanu ya yi masa ba ya san cewa shi masoyin Finafinan Indiya ne, wanda soyayyar ta sa da su ta fara ne tun kafin ya shigo a cikin masana'antar da ta yi sanadiyyar sanin sa da ki ka yi. Fadila, shi dai ra'ayi ba laifi ba ne, kuma shi ra'ayi riga ne kowa da irin na sa, kamar yadda kema ki ke da naki ra'ayin wanda wani ya fito fili wani kuma ke kawai ki ka bar wa zuciyar ki.

A ganina don Ali Nuhu ya kwaikwayi Finafinan Indiya ba laifi ba ne idan har labarin ya isar da sakon da ake so makallata su fahimta, idan kuma aka ga gyara sai ayi masa sharhi daidai da abin da aka kalla.

Kamata ya yi ace shawarar ce ki ka ba shi a kan ya rage kwaikwayo Finafinan Indiya yana yi masu kwaskwarima idan har gyara ki ke so ki yi masa, maimakon kudin goron da ki ka yi masa shi da abokin aikin sa wato Jarumi Adam A. Zango da ki ka bayyana su a matsayin masu shirin kashe masana'antar da ta suke neman abinci da ita, wanda babban kuskure ne ki ka tabka, na tabbatar babu yadda za a yi dan kasuwa ya kashe kasuwar sa madamar ba wata sana'ar ya samu ba, da kin yi bincike za ki san cewa shi kan sa Adamu Zango akwai babban jihadin da ya yi wanda wasu suka musulunta sakamakon fim din sa da suka kalla mai suna 'Ahlul Kitabi'

Fadila, ke kan ki kin yi watsi da al'adar Hausawan da ki ke tunkaho da su kuma ki ke kira da ikirarin cewa ke ita ce, ke kan ki kin dauki rayuwar turawa kin yi wa kan ki kallabi da dankwali kin yafa a jikin ki, domin ga dukkan wanda ya ke bibiyar ki zai ga cewa kin bi hanyar Dutsinma maimakon hanyar Kano da ki ke so ki dosa, duba da irin shigar turawar da ki ke yi wadda ta ke bayyana surar jikin ki a fili ba tare da sakaya jikin ki ba, a wasu hotunan da ki ke dorawa a kafofin soshiyal midiya da din ki.
Kin ga kenan kan ki ya kamata ki fara yi wa nasiha ta hanyar gyara shigar ki ki rinka yi ta kamala ta 'ya'yan Hausawa ki daina kwaikwayar shigar wasu kabilun ta yadda duk wanda ya gan ki zai ga tabbas cikakkiyar  Bahausa ce ba zai yi tunanin Ungozi ce ba ko kuma Chinyere!

Da kin so ki yi adalci a rubutun na ki na cikar shekarun Ali Nuhu 20 a masana'antar Finafinan Hausa, da sai ki fara bayyana irin tasirin sa da kuma nasarorin sa tare da dimbin mutanen da ya yi wa riga da wando a masana'antar kafin ki soke shi, wanda na tabbata idan ki ka yi haka ke da kan ki za a fahimci inda tsokacin na ki ya dosa maimakon fahimtar karatun bamaguje da ki ka yi wa cikar sa shekaru 20 a masana'antar.
Ko kina so ko ba ki so, jarumai irin su Ali Nuhu sun taimakawa Masana'antar fim sosai wadda har ta kai ga matsayin da ke a yanzu, sannan kuma ya taimakawa wasu daga cikin dimbin mutane da ke a masana'antar, wanda da kin yi dogon nazari kafin ki yi rubutun na ki ko shakka babu sai mun jinjina maki gami da taba maki sanadiyyar Gyara kayanka da ki ka yi kokarin yi.

Babban kuskuren ki da ki ka tafka a rubutun ki na cewa jarumai irin su Ali Nuhu su ne suke kokarin binne masana'antar Kannywood da kan su ta sanadiyyar Finafinan Indiya da suke kwaikwaya.

Zan so na kara maki haske da cewa mutuwar kasuwar Finafinan Hausa ba ta da alaka da irin Finafinan da ake shiryawa a masana'antar, saboda ko shekara 10 da suka gabata lokacin da ake rububin kallon Finafinan Hausa, da yawa daga cikin Finafinan da ake kallo akwai na Indiya din wadanda aka kwaikwaya, amma kuma aka ci gaba da ciniki tare da samun riba da harkar.

 Sannan ku kan ku masu kallo masu shirya Finafinan sun lura da cewa ko da an yi fim wanda ya ke nuna tsantsar al'adar Malam Bahaushe a cikin sa asara ake yi ba ta shi ki ke yi ba, an fi cinikin wanda ake rawa da waka, hakan yasa suke bin ra'ayin ku domin su kasuwanci su ke yi, kuma Bahaushe ya ce 'Don Lada ake Sallah.'

Babban abin da ya rusa masana'antar Finafinan Hausa, shi ne ZAMANI. Zamani ne yazo, su kuma 'yan fim suka ki bin zamanin, suka dogara da buga DVD suna kaiwa a kasuwar kofar wambai, suna sayarwa, irin kasuwancin da suka saba yi tun farkon kafuwar masana'antar, maimakon kai shi a tashohin Satilayit, da kuma silimu, sun kuma kasa kirkirar wata manhaja ta Intanet da za su rika sakin Finafinan ana kallo ana biyan su, maimakon buga shi a DVD da suka saba wanda ba kowa ba ne ke da lokacin da zai sayo kaset ya sanya gida ya kalla.

Wannan shi ne babban jigon mutuwar Finafinan Hausa, ba kamar yadda ki ka yi soki burutsu a alkamin ki ba wanda ya saba rubuta labari makamancin irin na su  Iliya Dan Mai Karfi.

Zan ci birki a nan ba don komai ba sai don jiran ci gaban rubutun ki kashi na biyu da ki ka ce za ki ci gaba, bayan kin kammala sai mu warware maki zare da abawa game da ita harkar fim din har ma da abin da ya kashe maku ita kan ta kasuwar ta ku ta Hadisan Kano. sannan ina mai baki shawarar da ki daina SHIGA SHARO BA SHANU.

Isah Bawa Doro

Drop Your Comment

0 Comments